Duniya ta kwallon kafa na alhini bisa rashin 'yan wasa da dama da suka mutu a hadurran mota, na baya-bayan nan shine tauraron Portugal, Diogo Jota, wanda ya rasu a Spain 'yan kwanaki bayan aurensa. Irin waɗannan hadurra sun yi sanadin mutuwar hazikai da dama, suna barin girgiza da bakin ciki a kulake, ga magoya baya da kuma ƙasashe.