Shugabannin Majalisun Jihohi 36 Sun Goyi Bayan Kafa Rundunar 'Yan Sandan Jihohi
Shugabannin Majalisun Dokokin Jihohi 36 a Najeriya sun bayyana cikakken goyon bayansu ga kafa rundunar 'yan sandan jihohi, suna mai cewa hakan zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro da suka addabi Æasar. Sun ce tsarin zai ba jihohi damar mayar da martani cikin sauri ga laifuka tare da inganta tattara bayanan sirri da tsaron al'umma.
Sun bayyana hakan ne yayin ci gaba da nazarin kundin tsarin mulkin Æasa, inda suka ce gyaran ya shiga matakin Æarshe. Sun kuma jaddada cewa dole ne a samar da Æa'idoji masu Æarfi da tsarin sa ido domin hana amfani da rundunar wajen tauye haÆÆin jama'a ko siyasantar da harkokin tsaro.
Idan gyaran kundin tsarin mulkin ya samu amincewar yawan majalisun jihohi da ake buÆata, Najeriya za ta samu babban sauyi a tsarin gudanar da harkokin tsaro.
Sharhi