NIGERIA TV INFO — TSARON DUNIYA
Trump Ya Ce An Kashe Jagoran Addinin Iran da Manyan Jami’ai 40 a Hare-haren Sama na Amurka da Isra’ila
Shugaban Amurka, Donald Trump, a ranar Asabar ya tabbatar da cewa an kashe Jagoran Addinin Iran, Ayatollah Ali Khamenei, tare da manyan jami’an soja da farar hula 40 na Iran sakamakon hare-haren sama da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran.
A cewar Trump, hare-haren sun nufi manyan shugabannin tsarin mulkin Iran, ciki har da manyan kwamandojin rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC). Ya kuma yi ikirarin cewa wasu daga cikin mambobin IRGC da suka tsira suna neman kariya daga Amurka bayan harin.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan babban farmaki na daga cikin mafi girman tashin hankali na soja a Gabas ta Tsakiya cikin ‘yan shekarun nan. A farkon ranar Asabar, sojojin Amurka da Isra’ila sun kai manyan hare-hare a muhimman wurare na Iran.
A sakon da ya aikewa da al’ummar Iran kai tsaye, Trump ya bukaci su “karbe makomarsu” ta hanyar tasowa su kalubalanci shugabancin addinin Musulunci da ke mulkin kasar tun 1979, lamarin da ke nuna goyon bayan sauyin gwamnati a Tehran.
Iran Ta Mayar da Martani a Fadin Gabas ta Tsakiya
A matsayin ramuwar gayya, Iran ta kaddamar da hare-hare kan kasashen da ke daukar bakuncin sansanonin sojin Amurka ko kuma ake kallonsu a matsayin kawancen Amurka a yankin. Kasashen da abin ya shafa sun hada da Saudiyya, Jordan, Qatar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Kuwait, Bahrain da Syria da sauransu.
Masana harkokin soja sun bayyana cewa Amurka na da kusan sansanonin soja 13 a Gabas ta Tsakiya, tare da sojoji kimanin 30,000 zuwa 40,000 da ake jibgewa a yankin.
Kamfanin dillancin labarai na duniya Reuters ya ruwaito cewa karuwar rikicin ta tilasta rufe wasu sassan sararin samaniyar Gabas ta Tsakiya, lamarin da ya haddasa tangarda ga zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa tare da kara fargabar illolin tattalin arziki da tsaro a duniya.
Yayin da rikicin ke kara kamari, kasashen duniya na sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa, tare da fargabar cewa rikicin na iya rikidewa zuwa cikakken yakin yankin da zai shafi duniya baki daya.
Sharhi