🔴 Firayim Minista na Isra’ila Netanyahu ya tabbatar da kaddamar da harin soja mai suna 'Rising Lion' da nufin “kawarda barazanar Iran ga wanzuwar Isra’ila.”
📣 Ya ce za a ci gaba da wannan aiki “har sai an cimma burin.”
💥 Bayan harin farko daga Isra’ila, Iran ta harba fiye da jirage marasa matuki 100 zuwa Isra’ila.
📢 Majiyoyin Isra’ila na cewa jiragen na iya ɗaukar awanni bakwai kafin su ketare Iraq, Syria, da Jordan zuwa Isra’ila.
📺 Talabijin gwamnatin Iran ya bayyana cewa jiragen kamikaze sun kai farmaki kan tsarin kariyar iska na Isra’ila. Wasu rahotanni sun ce an harba makamai daga sansanonin karkashin kasa a Iran – amma har yanzu ba a tabbatar da hakan ba.
📍An kai hari kan gidajen zama a Tehran, inda ake cewa hedkwatar IRGC ta kasance daya daga cikin wuraren da aka kai hari.
⁉️ Ana rade-radin cewa an kashe Janar Hossein Salami, kwamandan IRGC.
🔴 Rahotanni sun nuna cewa an kaddamar da harin daga sararin saman Iraq da ke karkashin ikon Amurka.
⚠️ Ginin makamashi na nukiliya a Natanz na ci da wuta – Iran ta tabbatar da cewa wuraren nukiliya biyu sun samu farmaki