Kamfanonin sadarwa ƙarƙashin ALTON sun ce umarnin da NIMC ta bayar na sauya zuwa sabon tsarin tantance shaida ya janyo katsewar ayyuka da suka shafi SIM a faɗin ƙasa. Sun tabbatar wa masu amfani da cewa ana ci gaba da kokarin dawo da ayyukan yadda ya kamata cikin gaggawa.