Hedikwatar Tsaro: Ba mu da ikon bayar da afuwa ga 'yan ta'adda

Rukuni: Labarai |

Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta bayyana cewa rundunar sojin Najeriya ba ta da ikon bayar da afuwa ga 'yan bindiga ko 'yan ta'adda da suka mika wuya. Wannan bayani ya fito ne daga Daraktan Harkokin Yada Labaran Tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, a matsayin martani ga rahotannin da ke cewa wasu shugabannin 'yan bindiga a Jihar Katsina na sakin mutane da suka yi garkuwa da su a matsayin musaya da alkawarin samun afuwa.