LABARI MAI ZAFI: SHUGABA TINUBU ZAI ZIYARCI JIHAR BENUE SABODA RIKICI, YA SAUYA ZIYARARSA TA KADUNA

Rukuni: Labarai |

Shugaba Bola Tinubu ya sauya shirin tafiyarsa zuwa jihar Kaduna, inda yanzu zai je jihar Benue a ranar Laraba, 18 ga Yuni, 2025. Wannan mataki na daga cikin kokarinsa na warware rikice-rikice da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi. A yayin ziyarar, zai gana da sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa, shugabannin addini, matasa da sauran masu ruwa da tsaki don samar da zaman lafiya da fahimtar juna. Kafin zuwansa, manyan jami’an gwamnati da suka hada da Sakataren Gwamnati, Sufeto Janar na ‘yan sanda, da shugabannin leken asiri sun rigaya sun isa don shirya karbar sa, alamar cewa gwamnati na daukar rikicin da muhimmanci.