Æungiyar Concerned Christian Youth Forum (CCYF) ta shirya gudanar da zanga-zangar lumana a ranar 21 ga Mayu a Unity Fountain, Maitama, Abuja daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana. Zanga-zangar na nuna rashin jin daÉin yadda ake Æara kai hari kan addinin Kirista da shugabanninsa.
Jagoran Æungiyar, James Paul Adama, ya ce suna zargin Omoyele Sowore da abokan aikinsa da ÆoÆarin tayar da rigimar addini. Ya ce, âAddininmu yana fuskantar barazana. Wannan shiri ne da aka tsara domin raba kan alâumma.â
CCYF na kuma neman gwamnati ta dauki mataki kan yawaitar kashe-kashe a Æasar. Za a samar da motocin daukar nauyin masu halarta daga sassa daban-daban na Abuja da Æananan hukumomi shida na FCT.
An bukaci matasan Kiristoci su halarta domin bayyana damuwarsu da kare imanin su.
Sharhi