Nigeria TV Info — Labaran Ƙasashen Waje
Wani shahararren mawaƙin ƙasar Mexico da aka sani da rera wakokin yabon shugabannin miyagun ƙwayoyi an harbe shi har lahira a cikin filin ajiye motoci a yammacin ƙasar, jami’an tsaro sun tabbatar da hakan da yammacin Talata.
Ernesto Barajas, babban mawaƙin ƙungiyar Enigma Norteño — wacce ke da fiye da masu sauraro miliyan huɗu a kowanne wata a Spotify — an harbe shi a garin Zapopan na jihar Jalisco.
Barajas shi ne na baya-bayan nan daga cikin fitattun mawaƙan narcocorridos, wani nau’in waƙar gargajiya mai cike da cece-kuce a Mexico da ke yabon ayyukan miyagun ƙungiyoyin dillalan ƙwayoyi, da aka kashe cikin ‘yan watannin nan.
Hukumomi na ci gaba da bincike game da lamarin kisan, wanda ya sake jaddada haɗarin da mawaƙa masu dangantaka da wakokin narcocorridos ke fuskanta.
Sharhi