Super Eagles na Najeriya sun fadi zuwa matsayi na 45 a sabuwar kundin darajar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na maza da FIFA ta fitar a ranar Alhamis, inda suka sauka daga matsayin da suke a baya da matsayi guda. Wannan koma baya ya kuma sa suka fita daga cikin manyan ƙungiyoyi biyar na nahiyar Afrika.
Rashin nasara a wasannin baya-bayan nan ne ya haddasa wannan koma baya. A Gasar African Nations Championship (CHAN), Eagles masu buga a gida sun sha kashi, yayin da babban tawagar ta yi ta fama a wasannin neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya — inda suka yi nasara da kyar akan Rwanda a Uyo sannan aka tashi canjaras tsakaninsu da Afirka ta Kudu.
Wannan sakamako mara kyau ya jawo musu raguwar maki a cikin lokacin bita, wanda ya bai wa Côte d’Ivoire damar yin gaba da su a tsarin darajar nahiyar.
Super Eagles, wadanda suka yi nasara da tagulla a gasar AFCON 2024, yanzu suna bayan Morocco, Senegal, Masar, Algeria da Côte d’Ivoire a jerin darajar nahiyar. Morocco har yanzu su ne na farko a Afrika, suna rike da matsayi na 11 a duniya bayan tarihi na zuwa matakin kusa da karshe a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022.
A gefe guda, Zimbabwe ita ce ƙasar da ta fi yin mummunan faduwa a duniya, inda ta sauka matsayi tara zuwa na 125. A matakin duniya, Spain ta hau kan gaba, ta maye gurbin Argentina wadda ta sauka zuwa matsayi na uku, yayin da Faransa ta tashi zuwa na biyu.
Sharhi